Babban kwamandan rundunar dakarun Amurka a Afirka wato AFRICOM Janar Macheal Langlay ya isa Najeriya ne a wata ziyarar aiki a kasar.
Da isarsa dai bisa rakiyar jakadan Amurka a Najeriya, kwamandan ya yi ganawar sirri da babban hafsan hafsoshin rundunar kasar Janaral Christopher Musa.
Babban hafsan hafsoshin Najeriyar ya nemi Amurkan da
ta dagawa Najeriya kafa musamman wajen gindaya tsauraran sharuddan sayarwa Afirka makamai, ganin a baya Najeriya ta yi ta cin karo da matsaloli sosai wajen shigo da makamai daga Amurka.
Da ya ke wa Muryar Amurka karin bayani kan wannan ziyara, kakakin rundunar tsaron Najeriya, Brigediya Janar Tukur Gusau ya ce biyo bayan zaben da akai wa Janar C. G Musa a matsayin shugaban kwamitin manyan hafsoshin tsaro na Afirka ta yamma, kan wannan Janar Langlay ya zo Najeriya don kara habaka dangantakar tsaro.
A cewar Janar Gusau, manyan Janar Janar din sun kuma tabo batutuwa kan yadda za a kara inganta alakar tsaro tsakanin Amurka da Afirka ta yamma.
Amurka a cewar Janar Gusau na da alaka mai karfi da dangantakar aikin soja da ta tsaro, tun da har makamai da kayan aiki da Najeriya ke saya daga Amurka ne.
Ya ce wani lokaci ma ko da kudinka sai an fuskanci matsaloli wanda hakan ke shafar aikin sojojin Najeriya a yakin da suke yi da ‘yan ta'adda, don haka ya nemi Janar Langlay da ya sa baki don shawo kan wannan matsalar.
Da yake tsokaci, wani masanin tsaro, Wing Commander Musa Isa Salman ya ce yana da kyau a fahimci tsarin da Amurka ke bi wajen sayarwa kasashe makamai, domin ko da baya ga rawar da sojoji ke takawa, ita ma majalisar Amurka na da ruwa da tsaki sosai.
Domin akwai al'amura wadanda suka shafi batun take hakkin bil'adama musamman daga jami'an tsaro, ko hare-haren da jami'an tsaron ke kaiwa dake shafar fararen hula da dai makamantansu, duk na daga cikin ababen da ake la'akari dasu.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5