Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Ukraine, Andriy Yermak, ya riga ya isa Amurka, kamar yadda ministan harkokin waje Andriy Sybiha ya shaidawa manema labarai a birnin Brussels, a cewar rahoton kamfani dillancin labaran Interfax na Ukraine.
“Wannan ganawa a matakin shugaban fadar shugaban kasa nada matukar mahimmanci domin kulla alaka, da wakilan sabuwar gwamnati,” kamar yadda Interfax ta Ukraine ta ruwaito sybiha yana cewa.
Har yanzu Trump bai yi karin haske akan shirinsa na kawo karshen mamayar watanni 33 ba, saidai tsare-tsare 3 da wasu makusantansa suka gabatar na ganin burin Kyiv na zama mamba a rundunar tsaro ta NATO ba zai yiyu ba.
Haka kuma mashawartan Trump na gabatar da wasu tsare-tsare da zasu sakarwa Rasha yankuna da dama, wacce ta mamaye kaso 1 bisa 6 Ukraine.
-Reuters