Wata kungiya mai kare ‘yancin matasa a jihar Kanon Najeriya da ke arewa maso yammacin kasar, ta ce a shirye take ta ba da gudunmuwarta domin ganin an yi zaben 2019 cikin lumana.
Kungiyar mai suna Kano Solidarity Organization a turance, ta ce ta dukufa wajen wayar da kan matasa da suka hada har da mata, dangane da muhimmancin zaben da zai kawo ci gaba ga al’uma a maimakon dabi’ar nan ta sayar da ‘yanci da wasu matasa ke yi a lokutan zabe, wacce ke haifarwa al’uma koma baya.
“Kokarin da muke yi shi ne akan matasa, a kowacce unguwa, muna kokari mu samu wanda yake kasuwa ko yake makaranta ko yake aiki da zai iya rika gamsar da wadanda ke kusa da shi.” In ji jami’in hulda da jama’a a kungiyar, Aliyu Ibrahim Saraki, yayin wata hira da ya yi da wakiliyar Dandalin VOA, Baraka Bashir.
Ya kara da cewa, a kullum abin da suke yi a kungiyoyinsu na matasa, shi ne fafatukar kwato ‘yancin kansu ta hanyar tabbatar da matasa sun samu ilimi mai inganci, ingata sana’oinsu da nisantar da matasa ‘yan ajin karshe daga illar shaye-shaye da bangar siyasa musammam ma a lokutan zabe.
A cewar Saraki, sun kafa kwamitoci a unguwanni da ke Kano wadanda suke ilmantar da matasa tare da kare kuri’un al’umma domin kaucewa zaben tumin dare.
Ya kara da cewa, babbar damuwarsu a yanzu ita ce, samar da mulkin da zai bai wa matasa ilimi, yana mai jaddada cewa, ilimi shi ne ginshinki ci gaban kowacce alumma a fadin duniya.
Your browser doesn’t support HTML5