Mika'il ya ce ya samo asalin sunan Gidigo ne shekaru 17 da suka wuce a wani fim, wanda ya ce ya fara fim ne tun yana jami’a a 1994.
Ya ce a wancan lokacin suna harkar fim ne a matsayin drama, inda wata rana ana makon Hausa suna tsaka da wasan ne, sai Dan Magori ya ga yadda yake wasan sa, sai ya neme shi tare da cewar lallai zai kawo sauyi a masana’antar fim.
Hanci ciki da parlour ya ce fim a wancan lokaci, zuwa wannan lokaci, akwai canji mai yawa. A da akwai ladabi da biyayya sabanin yanzu inda masana’antar ba ta da kofar shiga, babu kuma ka’idojin da ya dace.
Babban kalubalen da ya fuskanta a wancan lokacin shine, yadda al'ummar gari ke yi masa kallo, da wasu maganganu da yakan ji daga wajen mutane na zagi, da ire-iren makamantasu.
Ya ce harkar fim ya samu ci gaba masu yawa, domin kuwa fim ya yi masa komai, ciki har da yawon duniya, amma babban burinsa a tsaftace harkar fim, a sanya dokoki da ka’idoji domin inganta masana’antar.
Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5