Babban Bankin Najeriya Ya Sa Harajin Naira 6.98 Kan Hada-Hadar Kudi Ta Na’ura.

CBN

Babban bankin Najeriya ya sanya harajin Naira 6 da kwabo 98 kan hada-hadar kudi ta na’ura ga ‘yan kasar, wanda hakan ke nufin masu asusun bankuna zasu rinka biyan Naira 6 da kwabo 98 a duk lokacin da suka yi hada-hadar kudi ta na’ura ko wayan tarho daga ranar 16 ga watan Maris da muke ciki.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Babban Bankin kasar wato CBN da hukumar sadarwa ta Najeriya wato NCC suka rattaba wa hannu wanda aka raba wa manema labarai a yau.

Wannan lamarin wani bangare ne na yarjejeniya, da Babban Bankin Najeriya ya cimma da sauran bankunan kasuwanci, biyo bayan sabani da aka samu tsakanin bankunan da kamfanonin sadarwa kan hada-hadar kudi ta na’ura da sauran ayyukan tura sakonni da bankuna ke yi.

Kamar yadda sanarwar da Babban Bankin Najeriya ya fitar da hadin gwiwar hukumar sadarwa ta kasar, daga ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2021, za a fara cajar naira 6 da kwabo 98 a kan duk hada-hadar kudi ta bankuna da aka yi ta na’ura da sauran kamfanonin hada-hadar kudi masu lasisi a kasar, wanda hakan ke nufin wannan sabon harajin zai maye gurbin tsarin cajar kudi a kan kowanne hada-hadar kudi domin tabbatar da rage kudadden da masu asusun bankuna ke biya zuwa rabi don bunkasa fannin hada-hadar kudi.

Babban Bankin Najeriya dai ya ce, za a rinka yin wannan sabon tsarin a bayyane kuma zai tabbatar da cewa, ana cajar masu amfani da asusun bankuna haraji na bai daya ba tare da la’akari da adadin lokutan da suka yi hada-hadar bankuna ta na’ura ba inda babban bankin zai rinka cajar harajin na naira 6 da kwabo 98 kai tsaye daga bankunan masu asusun a madadin kamfanonin sadarwa domin tabbatar da an yi aiki a bayyane kuma bankunan kasuwa ba su da hurumin cajar karin haraji kan kwastamomin su kan hada-hadar kudi ta na’ura ba.

Kamar yadda Babban Bankin na Najeriya ya bayyana, an cimma matsaya kan sabon harajin ne wanda ya kasance wani bangaren yarjejeniya da aka cimma bayan ganawa tsakanin bankunan da kamfanonin sadarwa a jiya Litinin domin tattauna batun bashin da kamfanonin sadarwar kasar ke bin bankuna na Naira bilyan 42.

A cikin makon da ya gabata ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba wa kamfanonin sadarwar kasar umurnin dakatar da batun daina tsarin hada-hadar kudi ta na’ura tsakaninsu da bankunan kasar sakamakon bashin da su ke bin bankunan Najeriya.