Babban Abun dake Gaban Shugaban Nijar Shi Ne Samar wa Kasarsa Ababen More Rayuwa

Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou

A taron Majalisar Dinkin Duniya dake gudana yanzu a New York ta nan Amurka shugaban Nijar Mahammadou Issoufou yace babban abun da ya sa a gabansa shi ne samar ma al'ummar kasarsa ababen more rayuwa

Shugaba Mahammadou Issoufou yace duk da burinsa shi ne samar wa kasar ababen more rayuwa amma akwai matsalar tsaro da suke fama da ita kodayake ba kasarsa kadai take da matsalar ba..

Mahammadou Issoufou yace akwai bukatar kasashen da suka ci gaba su taimakawa kasashen dake tasowa yadda zasu yaki ta'addanci domin idan babu zaman lafiya to cigaba fa sai ta fatar baki.

Baicin zaman lafiya a dauki matakan bunkasa tattalin arzikin kasashen dake tasowa. Yace akwai abubuwa da yawa da yakamata kasashe masu hannu da shuni su taimakawa wadanda suke tasowa.

Shugaba Issoufou ya nuna kasar ba zata dogara ga man fetur ba kacokan amma zata gina tattalin arzikinta tare da gina dimokradiya mai dorewa. Daga karshe yace zasu cigaba da shirin nan da suka fito dashi na dan Nijar ya ciyar da dan Nijar.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Abun dake Gaban Shugaban Nijar Shi Ne Samar wa Kasarsa Ababen More Rayuwa - 2' 02"