Babban Abin Fargaba Ciwon Suga Ya Fara Kama Matasa

Wani kiyasi da hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO ta fitar ya nuna cewar akwai mutane miliyan dari uku da arba'in da shidda da ke dauke da wannan cuta ta suga a fadin duniya, kuma ko a shekara ta 2004 mutane miliyan uku da digo hudu ne suka rasu a sakamakon wannan cuta adadin da hukumar lafiya ta ce zai iya nunkawa kafin shekarar 2030.

Babban abin fargaba a cewar kungiyar masu dauke da wannan cuta ta duniya shine yadda cutar ke kama kananan yara 'yan kasa da shekaru goma sha biyar da yawan su yakai dubu saba'in ke kamuwa da nau'in farko na wannan cuta ta ciwon suga a duk shekara.

Ko ina mafita dangane da wannan cuta? tambayar da wakilin sashen Hausa babangida Jibrin yayi ma wani likita likitan hada magunguna a Najeriya inda ya bada bayani kamar haka, "yawancin magungunanda ake amfani dasu ga masu cutar ciwon suga ana amfani dasu ne domin a sami saukin radadin ciwon domin kada cutar ta kai wani matsayi da zata yi ma wanda yake dauke da ita lahani".

Likitan ya kara da cewa ba'a daukar wannan cuta kamar sauran cututtuka amma yanayin abinci da rashin motsa jiki musamman ga matasa kan iya sa wannan cuta ta kama matashi.

Ga cikakkiya hirar.