Ba'a San Makoman Gwamnatin Yemen Ba

'Yan Tawayen Houthi Shi'aYemeni suna tsaron hanyar da ta tafi fadar gwamnati a birnin Sanaa, kasar Yemen

Bayan da 'yan tawayen Houthi suka mamaye fadar gwamnatin Yemen babu wanda ya san makomar gwamnatin kasar

‘Yan Tawayen Houthi a kasar Yemen sun kwace ikon fadar shugaban kasa, kuma sun kaiwa gidan shugaban hari jiya Talata a birnin Sana’a, a hari na baya-bayannan akan shugabancin kasar.

Mayakan ‘yan darikar Shi’a sunyi arangama da jami’an tsaro, lamarin da ya keta yarjejeniyar tsagaita wuta na ranar Litinin da aka amince da shi, bayan da aka kashe mutane 9 a babban birnin kasar.

A wani jawabi da ya bayar ta gidan telebijan, shugaban ‘yan tawaye Abdel Malik Al Houthi yace kungiyarshi na gwagwarmayar kawo karshen cin hanci da rashawa ne, da kuma mulkin kama karya a duk fadin kasar. Bai umarci cewa gwamnati ta sauka ba, amma yayi gargadin cewa zasu iya daukar matakai nan gaba.

Har yanzu ba’a san inda shugaba Abd Rabbuh Mansour Hadi yake ba, amma wani jami’i ya bayyana cewa shugaban na cikin gidanshi cikin koshin lafiya.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yayi kira a kawo karshen takaddama, harma ya nemi a mayarwa gwamnati cikakken ikonta. Biyo bayan kiran wani taron gaggawa na kwamitin sulhu a Majalisar Dinkin Duniya jiya Talata, jami’an diflomasiyya sunyi Allah wadai da tashe-tashen hankulan, inda suka nemi a samar da yarjejeniyar zaman lafiya na dun-dun-dun.

Mayakan Houthi masu neman a karawa ‘yan Shi’a wadanda basu da rinjaye ‘yanci, sune suka kwace ikon babban birnin a watan Satumba.

SAUTI: Ba'a San Makomar Gwamnatin Yemen Ba - 0" http://bit.ly/1ukeYOJ

HOTO: 'Yan Tawayen Houthi Shi'a

#Hausa #Yemen