Shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasar Sifaniya, Luis Rubiales, ya yi amai ya lashe bayan da ya sauya matsayarsa ta cewa zai yi murabusa daga mukaminsa, inda ya jaddada cewa ba zai ajiye aikin nasa ba har sai inda karfinsa ya kare.
Rubiales ya furta hakan ne duk da kurar da ya tayar bayan sumbatar wata ‘yar wasan kasar da ya yi a labbanta ba tare da amincewarta ba a lokacin da Sifaniyar ta lashe kofin gasar mata ta duniya.
Rubiales ya sumbaci Jenni Hermoso, zakarar gasar cin kofin duniyar a labban ta lokacin da ake bikin raba kyaututtuka a Sydney babban birnin Australia a ranar Lahadi, bayan da Sifaniyar ta doke Ingila da ci daya da babu a wasan karshe na gasar cin kofin Duniyar ta mata.
Wannan lamarin ya haifar da suka daga ciki da wajen Sifaniya inda ministocin gwamnati, ‘yan wasa da masu horar da su, suka nemi da ya ajiye aikinsa.
Kafofin yada labaran Sifaniya sun ruwaito cewa Rubiales zai ajiye aiki kuma ana sa ran cewa zai yi hakan a wurin wani taron kolin gaggawar da kungiyar kwalon kafar ta kira a yau Jumma’a.
Sai dai bayan da ya fito ya ba da hakuri a bisa abin da ya aikata, Rubiales ya ki mika wuya bori ya hau, inda a karshe ya nanata cewa, “ba zan ajiye aiki ba”.