Gwamnan jihar Virginia, Ralph Northam, ya nanata matsayarsa ta cewa, ba zai sauka daga mukaminsa ba, kan wani hoto da ya bulla, wanda aka dauka tun lokacin yana makaranta, wanda ya nuna shi a matsayin mai akidar wariyar launin fata.
Hoton ya nuna wani mutum shafe da bakin penti a fuskarsa, yana tsaye a kusa da wani mutum sanye da fararen tufafin da masu kishin farar fata na ‘yan kungiyar Ku Klux Klan ke sakawa.
Yayin wani tsokaci da ya yi ga manema labarai a jiya Asabar, Northam ya musanta cewa yana daya daga cikin mutanen da ke cikin wannan hoto.
Ya kuma ce shi bai sayi kundin hoton daliban da ke dauke da wannan hoton ba, wanda aka wallafa a shekara 1984, inda ya kara da cewa, shi bai ma san cewa akwai hoto mai kama da wannan ba, sai a jiya Juma’a.
Gwamnan na jihar ta Virginia, ya ce sun dukufa shi da ma’aikantansa, domin su kafa hujjar cewa ba shi ba ne a cikin wannan hoto.
Sai dai Northam ya amince cewa lallai a lokacin yana dan shekaru 25, ya yi wata shiga inda ya shafa bakin penti a fuskarsa a lokacin wata gasar rawa da aka yi a San Antonio na jihar Texas.
A lokacin gasar, Notharm ya ce ya fito a matsayin shahararren mawakin nan ba'amurke dan asalin Afirka, wato Michael Jackson, lamarin da ya ce ya yi da na sanin bai yi ba.