Ba Za Mu Taba Sayar Da Mbappe Ba – PSG

Dan wasan PSG Kylian Mbappe - (SOCCER-FRANCE-MPL-PSG/REPORT Kylian Mbappe)

Dan shekara 22, Mbappe wanda ya zura kwallo 42 a gasa daban-daban a kasar ta Faransa, yana da kwangila da PSG wacce za ta kare a watan Yunin 2022.

Shugaban kungiyar Paris Saint Germaine (PSG) Nasser Al- Khelaifi, ya ce ba za su taba saka dan wasansu Kylian Mbappe a kasuwa ba.

Al- Khelaifi ya yi wannan tsokacin ne bayan jita-jita da take ta yawo a kafafen sada zumunta, wacce ke cewa suna shirin sayar da Mbappe.

“Ba za mu taba sayar da shi ba, kuma ba zai tafi a matsayi na gashin kansa ba ba tare da an sayar da shi ba,” In ji Al-Khelaifi, kamar yadda shafin Sky Sport ya ruwaito Reuters na cewa.

Al-Khelaifi ya ce, Mbappe babu abinda ya rasa, kuma Faransa kasar ce, saboda haka, “ina zai je?

Dan shekara 22, Mbappe wanda ya zura kwallo 42 a gasa daban-daban a kasar ta Faransa, yana da kwangila da PSG wacce za ta kare a watan Yunin 2022.

An yi ta rade-radin zai koma Real Madrid a gasar La Liga.

Al-Khelaifi wanda ya yi asalin hirar da jaridar L’ Equipe ya ce, yana fatan Mbappe zai kare rayuwar kwallonsa a kungiyar.

Kazalika ya ce, ba su da niyyar sayar da Neymar duk da cewa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, na kokarin sake sayen shi.