Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi tir da yunkurin juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar, yana mai cewa “duk wani yunkuri na hambarar da gwamnatin dimokradiyya ba bisa ka’ida ba, abin a kyamace shi ne, kuma abu ne da ba za a lamunta ba a duniya.”
Buhari ya yi magana ta wayar tarho da takwaran aikinsa na Nijar, Mahamadou Issoufou da ke shirin kammala wa’adin mulkinsa, inda ya jajanta masa bisa wannan al’amari.
Karin bayani akan: Mahamadou Issoufou, Shugaba Muhammadu Buhari, Mohamed Bazoum, Mahamane Ousmane, Jamhuriyar Nijar, PNDS, Nigeria, da Najeriya.
Najeriya dai makwabciya ce ga Nijar kuma abokiyar hulda ta kud-da-kud.
Shugaban na Najeriya ya kuma yi gargadin cewa, kasashen duniya ba za su lamunta da duk wani sauyin gwamnati ta hanyar amfani da karfin tuwo ba, abin da ya ce ba shi da hurumi a kundin tsarin mulki.
Kalaman na Buhari, wanda yanzu haka yake London don ganin likitocinsa, na kunshe ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan huldar yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.
“Tsabar nuna rashin kwarewa ne a yi yunkurin kawar da gwamnati da karfin gaske. Ya kamata sojoji da ke katsalandan a harkokin siyasa, su rika girmama zabin mutane da kundin tsarin mulkin kasa,” shugaban na Najeriya ya fada a cikin sanarwar.
Buhari ya kara da cewa ya damu matuka da irin mummunan tasirin da juyin mulki zai yi ga zaman lafiya da ci gaban nahiyar Afirka.
“Najeriya ba za ta zura ido tana kallon irin wannan barazana na faruwa a Afirka ba. Juyin Mulki ya zama tsohon yayi, kuma mu san da cewa, katsalandan din da sojoji ke yi a harkokin siyasa ta hanyar amfani da karfi don sauya gwamnati, na yin illa ne ga nahiyar Afirka.” In ji Buhari.
Shugaban na Najeriya, ya kuma yi kira ga shugabannin nahiyar Afirka da “su hada kai wajen yakar dabi’ar juyin mulki ko ya take,” yana mai gargadin cewa, “ya kamata masu juyin mulki su koyi darasi daga tarihi, kan sakamakon da ke biyo bayan haifar da hargitsi, sanadiyyar amfani da karfi wajen kifar da gwamnati.
Buhari ya kuma yabawa jami’an tsaron kasar ta Nijar da suka murkushe wannan bore da masu juyin mulkin suka so su yi wa zababbiyar gwamnatin Jamhuriyar Nijar.
Yadda Gwamnatin Nijar Ta Dakile Yunkurin Juyin Mulki
Your browser doesn’t support HTML5