A cewar Lamido ba lallai ba ne shugabannin da za su yi taro a kan haka su gane yaya matsalar yunwa ta ke tun da ba su santa ba.
“A lokacin ina ministan harkokin waje, da za mu je wani taro a nan Afrika kan matsalar yunwa da talauci da yake-yake da rashin lafiya da kuma yadda za a inganta rayuwar mutane. To mafi yawanci idan ana irin wannan taro, za ka ga cewa mu da muke wurin da yanayin mutanen da ke wajen da irin abincin da ke wurin, da wuya ka fahimci menene yunwa ko kuma talauci.” In ji Lamido.
Ya kara da cewa “saboda haka a wajen shugabancin mutane, idan kana magana akan abin da yake damunsu da bukatunsu, ka ji abin a ra’ayin su bakinsu.” Shi ne za ka iya magance matsalar.
Ya kara da cewa kamata ya yi a kira wadanda lamarin ya shafa sai su maka bayani kan yadda ya ke jin matsalar, “kai kuma sai ka yi amfani da iliminka da kwarewar ka wajen tunkarar wadannan abubuwan.”
Game da nasarar da APC ta samu a jihar ta Jigawa, Lamido ya ce gwamna mai zuwa, mulki zai yi na ‘yan Jigawa ba mulki na APC ba.
“Zabe hanya ce kawai ta kaiwa ga mulki, idan kuma ka ci zaben, mulkin na jama’a ne, saboda haka yanzu Jigawa ce APC sa.”
Ga karin bayani a hirar wakilin Muryar Amurka Mahmud Kwari da Gwamna Sule Lamido:
Your browser doesn’t support HTML5