Shugaban yana wa ‘yan jarida tsokaci ne game da wani harbin da wasu suka bayyanna na ganganci da akayi wa wasu bakaken fata Amurkawa anan Amurka a cikin ‘yan kwanaki biyun da suka gabata.
Wannan harin dai ya sake tada wata alamar tambaya akan irin yadda ‘yan sanda ke wuce gona da iri wuri a aikin su musammam ga tsiraru.
Da sanyin safiyar yau Juma'a ne dai Obama yake wannan Magana, jim kadan da saukar sa Warsaw, Poland inda zai halarci taron NATO.
Yace yakamata duka Amurkawa su nuna damuwar su game da wannan aika-aikan na yadda ‘yan sanda suke harbin bakaken fata, wanda yake kara aukuwa.
Shugaba Obama ya kira wannan nuna tsananin banbanci musammam akan tsarin shari'ar kasar Amurka, yace wannan banbanci kuma kididdiga ya nuna cewa Amurkawa bakake da ‘yan Latino suna ganin banbanci daga wurin ‘yan sandan kasar.
Yace da zaran irin hakan ta faru, da yawan Amurkawa sukan rika jin cewa ana yi wa bakake haka ne sabo da launin jikin su, ba a daukar su daya da sauran jama'ar kasar farare ba, wannan abin kuma yana bata rai kwarai da gaske.
Yayinda yake jawabi a Poland sai gashi a biranen Dallas da Washington DC bakake na zanga zangar kin jinin 'yansandan. A Dallas ma 'yansanda goma aka harba kuma tuni uku daga cikinsu suka rigamu gidan gaskiya.