Ba Ni Da Wata Alaka Da Shirin N-Power – D’Banj

D'Banj (Facebook/D'Banj)

A ranar Laraba hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa da ayyukan da suka shafi almundahana a Najeriya, ta ce ta tsare mawakin inda ta bincike shi kan zargin hannu a wata badakalar shirin na N-Power da gwamnatin Muhamamdu Buhari ta kirkira a 2016.

Mawakin Najeriya, Oladapo Oyebanji, wanda aka fi sani da D’Banj, ya musanta rahotanni da ke nuna cewa an samu hannunsa a wata badakala da ta shafi wawure kudaden shirin rage talauci na N-Power da gwamnati ta kirkira.

A ranar Laraba hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa da ayyukan da suka shafi almundahana a Najeriya, ta ce ta tsare mawakin inda ta bincike shi kan zargin hannu a wata badakalar shirin na N-Power da gwamnatin Muhamamdu Buhari ta kirkira a 2016.

Sai dai a wata sanarwa da lauyar D’Banj Maryam El Yakubu Musa ta fitar a madadinsa, mawakin ya musanta hannun a wata badaka da ta shafi N-Power.

“D’Banj ba shi da wata alaka ko wani kwantiragi da wata kungiya ko wasu mutane a ciki ko wajen gwamnati da ta shafi batun tafiyarwa ko raba kudaden da suka shafi mallakar wata hukumar gwamnati.” In ji sanarwar lauyar tasa.

Ko da yake, mawakin ya amince cewa ya je ofishin hukumar a ranar Litinin a Abuja, inda aka ce masa ya koma ranar Talata, saboda yamma ta yi a ranar.

“Muna da kwarin gwiwar cewa, kwakkwaran binciken da hukumar ICPC za ta gudanar zai wanke shi nan ba da jimawa ba.”

Rahotanni sun yi nuni da cewa ana zargin D’Banj da hada kai da wasu jami’an gwamnati inda aka kirkiri sunayen boge a jerin wadanda za su amfana da tallafin na N-Power.

Bayanai sun yi nuni da cewa, an bi diddigin kudaden da aka biya wadannan sunaye na boge, an kuma gano asusun mawakin suka shiga.

Sai dai D’Banj ya musanta wadannan zarge-zarge, yana mai cewa bayanan da aka wallafa akansa, yunkuri ne na neman a bata masa suna, yana mai jaddada cewa, nan ba da jimawa ba, gaskiya za ta yi halinta.

Wata sanarwa da ma’aikatar ayyukan jin-kai ta tarayya a Najeriya ta fitar a ranar Laraba, ta ce ita ta shigar da kara a gaban hukumar ta ICPC bayan da ta samu korafe-korafe.

“Mun samu labarin cewa, an gayyaci wasu mutane don a gudanar da bincike.” In ji ma’aikatar jin-kan.