Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye na Senegal ya ba kowa mamaki kan umurnin da ya bayar da ba a saba ji ko gni ba, inda ya bayyana cewa, baya bukatar taryar duk wani jami'in soja ko farar hula a filin jirgin sama a lokacin tafiya ko dawowar shi gida daga tafiya.
Hakan dai ya nuna a fili cewa shugaban na Senegal mai shekaru 40 a duniya wanda a kwanan nan ne aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar, baya bukatar wani abu mai kama da dan kwarya kwaryan biki da bisa al’ada akan yiwa shugabn kasa a filin jirgin sama a duk lokacin da zai yi tafiya, wato yan rakiya, ko kuma masu tarya idan ya dawo.
Shugaba Faye na bukatar irin wannan al’amari ya zama cikin sauri kuma cikin sauki.
Ya nuna a fili baya bukatar a tattaro mishi manyan mutane a gwamnati ko wani bangare domin kawai su tare shi ko suyi mai rakiya a filin jirgin sama.
Acewarsa jami'in gwamnatin na da aiyukan da ya kamata su maida hankali akan su maimakon yi mi shi rakiya ko tarbar shi.
Shugaban na Senegal ya zabi a shiga filin jirgin saman ba tare da wani kace nace ba. Ba wani jerin gaishe gaishe ko wani biki. Da ga shi sai abokan tafiyar sa kawai.
Wannan tsarin na shugaba Faye dai tsari ne da iya cewa yazo a zamanance kuma wanda za a iya aiwatar da shi wanda ya nuna a zahiri cewa, shugaba ne wanda ya kula sosai da muhimmancin lokaci da yin amfani da shi ta hanyar da ta dace.
Kuma ya nuna shi ba kyale-kyale ne a gaban shi ba, kuma ba sai anyi mi shi hakan ba ne zai san cewa lallai ya isa.
Da yawa ana kallon wannan mataki na sabon shugaban a matsayin sabuwar hanya mai sauki da mutuntawa, kuma kyakkyawan abin koyi ga sauran shugabanni.