Ba Mu Zuwa Makaranta Idan Aka Yi Ruwan Sama

Makarantu da dama a jahar Kano, na fuskantar matsaloli da dama wadanda suka hada da rashin zuwan dalibai makarantar musamman lokacin ruwan sama, ko damina.

A wata hira da wakiliyar dandalin VOA ta yi da wasu yara 'yan makaranta, sun bayyana mata cewar iyayen su ne suka hana su zuwa makarantar duk da kuwa ranar aiki ce ya kamata a ce yaran suna makaranta a wannan lokacin.

Da ta nemi jin ta bakin wasu daga cikin iyayen yaran, sun koka ne musamman dangane da yadda wasu lokuta idan aka yi ruwan sama yaran kan dawo gida da jikin su a jike idan aka yi ruwan sama. kuma sun kara da cewar wani lokaci idan ruwa ya bugi yaran yakan sakar masu zazzabi.

A cikin wasu daga cikin malaman da suka nemi a skaya sunan su, sun bayyana cewa wasu dalilan da suka sa hakan wadanda a ciki akwai rashin muhalli sosai.

A cewar ta "azuzuwan na zuba idan aka yi ruwan sama, kuma wasu malamai da dama sukan ki zuwa aiki."

Ga rahoton Baraka Bashir

.