Ba Mu Yi Zaben Tumun Dare Ba A Nada Ganduje Shugabancin APC - Fadar Aso Rock

An nada tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugabancin jam'iyyar APC.

Fadar shugaban Najeriya ta Aso Rock ta ce ba ta yi zaben tumun dare ba a nada tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC.

Ganduje ya zama shugaban jam'iyyar APC ne bayan da aka share makonni ana yada jita-jitar nada shi mukamin.

A wani taron majalisar koli na APC a karkashin jagorancin shugaba Tinubu, APC ta ayyana Ganduje a matsayin wanda ya maye gurbin tsohon shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu.

Mai ba shugaban Najeriya shawara kan siyasa Ibrahim Kabir Masari, ya ce gogewar tsohon gwamnan kan dabarun siyasa su ka duba wajen dora shi kan kujerar.

Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

Tun fitowar labarin rade-radin ba Ganduje mukamin aka yi ta tafka muhawara tsakanin masu mara baya da akasin hakan, har ma a cikin jam'iyyar.

Daraktan yada labaran jam'iyyar Bala Ibrahim ya ce irin wannan cece-ku-cen ba sabon abu ba ne a siyasa.

A yanzu dai za a zuba ido a ga tasirin da tsohon gwamnan zai yi kan mukamin bayan samun targade a zaben dan takararsa na gwamnan Kano Nasiru Gawuna wanda Abba Kabir Yusif na jam'iyyar NNPP ya yi nasara a kansa.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Mu Yi Zaben Tumun Dare Ba A Nada Ganduje Shugabancin APC - Fadar Aso Rock