Ba Mu Kori Rahama Dalilin TikTok Ba - Hukumomin Makaranta

Rahama

Wani batu da ya ja hankalin 'yan Najeriya a kwanannan shi ne na wata daliba da aka kora daga makarantar nazarin kimiyar ayukkan jinya da ungozoma ta jihar Kebbi, da sunan cewa tana badala a dandalin sada zumunta na yanar gizo na Tiktok.

SOKOTO, NIGERIA - To sai dai bayanin da makarantar ta fitar ya sha bamban da wanda ake yadawa na cewa an kore ta saboda tana Tiktok ba.

Makarantar Rahama

Bayanai da hotonan wata yarinya mai suna Rahama Sa'idu sun karade kafar zada zumunta ta facebook, wadda aka ce an kora daga makarantar nazarin ayukkan jinya da ungozoma ta jihar kebbi saboda tana aikata ayukkan rashin kunya da tarbiya a kafar sada zumunta ta Tiktok.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin yarinyar, sai dai abin ya ci tura, amma a wani faifan bidiyo da ta saki ya nuna tana nadama akan korar ta da aka yi daga makaranta, kuma yanzu bata san ta ina zata soma ba.

To sai dai bayanin da makarantar ta fitar ya sha bamban da zancen da ake yadawa a soshiyal midiya na cewa an kore ta saboda nuna tsiraici da badala a kafar Tiktok.

Takardar Makarantar Rahama

Shugaban makarantar Muhammad Murtala Musa ya ce yarinyar wadda ke karatun aikin ungozoma, tun tana ajin farko a makarantar ta fadi jarabawa aka kara mata wata shida ta gyara jarabawar ta, ta gyara ta wuce aji na biyu, nan ma a zangon karatu na biyu ta fadi jarabawa aka sake bata wata shida ta gyara amma daga nan ba a kara ganin ta ba har wata hudu.

Ya ce matsalar dalibai biyu ne ta shafa kuma hukumar makaranta ta basu takardar gargadi akan kauracewa makaranta har tsawon wata hudu, kuma dukan daliban sun bayar da jawabi na rashin zuwan su, makarantar ta nemi su hadu da kwamitin ladabtarwa na makarantar.

Yarinyar ta fuskanci kwamitin amma ita Rahama ta ki ta zo, aka kara mata sati biyu, kuma ta ki ta zo, daga nan kwamitin ya kori dukan yaran biyu.

Takardar bayanin Rahama

Dangane da batun korar Rahama saboda tana Tiktok, shugaban makarantar ya ce ba su ma san tana amfani da kafar sada zumunta ta yanar gizo ba, kuma koda sun san tana yi, damar ta ce ta yi abinda rayuwar ta ke so.

Kungiyoyin fafatukar kare hakkin mata sun nuna rashin jin dadi akan faruwar wannan lamari.

Shuagban kungiyar kare hakkin mata ta' WRAPA' a jihar Kebbi Nasir Idris ya ce abin haushi ne aikata abinda zai kai ga korar daliba mai karatun fannin kiyon lafiya musamman duba da yadda ake bukatar samun mata a wannan fannin.

Ya ce kuma wannan ya zama darasi ga dalibai su kasance masu biyayya ga umurnin makaranta da himma ga karatu, su kuwa iyaye su kasance masu kula da karatun 'ya'yansu.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Mu Kori Rahama Dalilin TikTok Ba - Hukumomin Makaranta.mp3