Ba Mu Karaya Ba A Yunkurinmu Na Lashe Kofin Premier - Arteta

Arteta

Arsenal ta sha kaye a hannun Manchester City da ci 4-1 a makon da ya gabata yayin da take shirin karawa da Chelsea a ranar Talata.

Kocin Arsenal Mikel Artata, ya ce tawagar ‘yan wasansa ba ta gamsu da nasarar da ta samu ta shiga rukunin kungiyoyin da za su kara a gasar Champions League ba, yana mai cewa, za su ci gaba da fafatawa don neman lashe kofin Premier na bana.

Arteta ya ce, “irin kwarin gwiwar da suke bukata kenan a yanzu, musamman kwanakin karshe da suka rage kafin kammala gasar.”

Arsenal ta sha kaye a hannun Manchester City da ci 4-1 a makon da ya gabata yayin da take shirin karawa da Chelsea a ranar Talata.

Chelsea dai na ta taga-taga a gasar ta Premier ta bana.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito Arteta yana cewa “abubuwa da dama za su faru” a fafatukar neman lashe kofin gasar ta Premier a bana.

Mutane da yawa dai na ganin City ta riga ta lashe kofin a bana.