Ba Mamaki 'Yan-Tawayen Houthi Da Gwamnati Su Dai-Daita

Wani mai magana da yawun 'yan tawayen Houthi ya ce, mai yiwuwa 'yan tawayen su amince da cigaba da tattaunawa da gwamnatin da su ke jayayya da ita. Muddun komai ya tafi dai dai a tattaunawar da ake yi a kasar Sweden.

Mai magana da yawun kungiyar Houthi, Mohammed Abdelsalam ya ce, “Idan an samu cibaga a tattaunawar da za mu yi, wato cigaba wajen samun yarda da juna cikin aminci, da kuma tsarin da za a bi, za mu iya cigaba da wasu zagaye na tattaunawar" cikin watanni masu zuwa.

Wasu abubuwan da aka tabo a tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ke daukar nauyin shiryawa, su ne musayar fursunoni da sake bude filin jirgin sama na Sanaa.

Wasu rahotanni sun ce bangarorin biyu sun amince da musanyar fursunoni kafin tattaunawar da za’a yi a Stolkham, amma, ba a sami wani cigaban kwarai ba akan wasu batutuwan.

Kamar batun bude filin jirgin saman Sanaa, da iko akan tashar jirgin ruwa na Hodeidah wanda shi ne mafi girma a kasar Yemen.