Ba Inda Messi Zai Je, Yana Nan Daram A Barcelona - Bartomeu

  • Murtala Sanyinna

Lionel Messi

Shugaban kungiyar kwallon kafar Barcelona ta kasar Spai Josep Bartomeu, ya musanta rahotannin da ke bayyana cewa shahararren dan wasan kungiyar Lionel Messi, na kan hanyarsa ta barin kungiyar a shekara mai zuwa, idan kwantaraginsa ya kare.

Bartomeu ya jaddada cewa “ba inda Messi zai je, domin ko dan wasan ya bayyana hudurinnsa na karkare rayuwarsa ta kwallon kafa a kungiyar.”

Lionel Messi

An yi ta samun rahotannin da ke cewa dan wasan dan kasar Argentina na barazanar barin kungiyar ta Barcelona, sakamakon rashin gamsuwa da yadda al’amura ke gudana a kungiyar, kazalika da kuma takun saka tsakaninsa da shugaban kungiyar Bartomeu, lamarin da ya sa ya dakatar da duk wata tattaunawa akan sabunta kwantaraginsa a kungiyar.

To sai dai wannan ne karon farko da shugaban kungiyar Bartomeu ya yi sharhi akan lamarin, yana mai tabbatar da cewa dan wasan na da bukatar ci gaba da zamansa a Nou Camp.

Josep Bartomeu

Duk da yake wasu rahotannin sun ce an dade ana tattaunawa tsakanin shugabannin kungiyar da mahaifin Messi, to amma har kawo yanzu dan wasan mai shekaru 33 bai kai ga rattaba hannu a wani sabon kwantaragi da kungiyar ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Abubuwan Bajinta Biyar Da Har Yanzu Lionel Messi Ke Zarra Kai