Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ba da saninsa ya taka hoton tsohon gwamnan jihar Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ba sabanin yadda rahotonni ke nunawa.
A karshen makon da ya gabata, an ta yada wasu hotuna wadanda suka nuna Gwamna Ganduje ya taka hoton Kwankwaso.
Lamarin ya faru ne a taron gangamin da jam’iyyar APC ta shirya na karban wasu mambobin Kwankwasiyya da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki.
Lamarin ya janyo suka daga jama’a da dama a ciki da wajen jihar ta Kano wacce ke yammacin arewacin Najeriya.
Sai dai wata sanarwa da Kwamishinan yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Litinin, ta kare gwamna Ganduje inda ta ce ba da saninsa ya taka hoton ba.
Karin bayani akan: Abdullahi Umar Ganduje, APC, Nigeria, da Najeriya.
“Wani hoto da ya karade shafukan sada zumunta wanda ya nuna Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana taka hoton tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso a wani taron gangamin APC, ba da gangan ba ne, kuma ba shiryawa aka yi ba.”
“Duk da irin rashin jituwa ta fuskar siyasa da ke faruwa, ba halin Gwamna Ganduje ba ne ya nuna rashin girmamawa ko ya kaskantar da wani shugaban siyasa.” Garba ya kara da cewa.
A cewar kwamishinan, “a lokacin da aka kira Gwamna Ganduje don ya yi jawabi, tsoffin mambobin Kwankwasiyya sun jeru a gefe don su nuna mubaya’a ga gwamnan, wasu daga cikinsu sun yi ta watsi da hoton tsohon gwamnan, inda daya daga cikin hotunan ya fadi akan jar shimfidar da aka yi wa gwamnan don ya wuce, sai ya taka hoton ba tare da ya sani ba.” Kwamishinan ya kara da cewa.
A cewar Garba, wasu da ba sa son zaman lafiya ne suka sauyawa lamarin fuska, don su cimma wani burinsu.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka yi bikin zagayowar ranar dimokradiyya, inda wasu tsoffin ‘yan takarar mukamin gwmana biyu da dumbin magoya bayansu suka sauya sheka zuwa APC.