A hirar shi da Muryar Amurka, masani a fannin sufurin jiragen sama , Kyaftin Bala Jibrin Muhammad, ya ce ababen da ka iya jawo faduwar jirgin sama sun banbanta, kuma ba zai yi wu musababbin samfurin kirar jirage daban-daban su zama daya ba.
Shi ma a nashi bayanin, masanin sufurin jiragen sama, kyaftin Muhammad Joji, ya bayyana cewa, abun lura shi ne mafi kyawun hanyar sufuri mara yawan hadura shi ne sufurin jiragen sama a duk duniya yana mai cewa, an fi yawan hatsari a tafiya da motoci a kan jiragen sama.
A ranar 21 ga watan Febrairu da mu ke ciki ne karamin jirgin saman fasinjoji na rundunar sojin saman Najeriya ya yi hatsari a kusa da filin tashi da saukar jiragen saman birnin Abuja sakamakon matsalar injin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7 da ke ciki.
Rundunar sojin saman Najeriya dai ta fara bincike don gano musababbin hatsarin jirgin saman kirar Beechcraft King Air 350i, wanda ke kan hanyar dawowa birnin Abuja bayan gano cewa injin sa ya samu matsala a lokacin da hatsarin ya faru.
akalla-soja-guda-ne-ya-mutu-a-hadarin-jirgin-saman-da-ya-auku-a-abuja
mutuwar-kobe-bryant-ta-kada-mutane-da-yawa
kamfanin-boeing-ya-dakatar-da-sayar-da-samfurin-jirgin-max
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5