Ba'amurke Ya Zama Kocin Super Falcons Ta Najeriya

  • Murtala Sanyinna

Kungiyar Super Falcons ta Najeriya.

Hukumar kwallon kafar Najeriya - NFF, ta nada dan kasar Amurka, Randy Waldrum, a matsayin mai horar da tawagar ‘yan wasanta mata na Super Falcons.

Waldrum ya yi aikin horar da ‘yan wasan kasar Trinidad and Tobago tsakanin shekarun 2014 zuwa 2016.

A yanzu zai maye gurbin dan kasar Sweden Thomas Dennerby, wanda ya kasa kai kungiyar ta Super Falcons ga samun tikitin shiga gasar wasannin Olympics ta shekarar nan ta 2020 a birnin Tokyo ta kasar Japan.

Kungiyar Super Falcons ta Najeriya

Shugaban hukumar ta NFF Amaju Pinnick ya fada a wata sanarwa cewa, ya ji dadin samun kocin, inda kuma ya bayyana yakinin cewa sabon shugabancin kungiyar zai daga martabar ta da lamurran wasannin kasar baki daya.