Ba Aikin 'Yansanda Ba Ne Sun Shiga Harkokin Zabe ko Su Binciken Takardun Ababen Hawa

IBRAHIM K. IDRIS babban sifeton 'yansandan Najeriya

Sabon mataimakin babban sifeton 'yansandan Najeriya mai kula da shiya ta goma sha daya da ta hada da jihohin Ondo da Ogun Mr. Dan Bature ya gargadi 'yansanda cewa duk wani jami'insu da aka samu da hannu dumu dumu a harkokin yakin neman zabe zai dandana kudarsa

Musamman a lokacin zabe idan aka samu wani dansanda da hannu cikin taimakawa wani dan takara a lokacin zabe to ko shakka babu zai yabawa aya zaki.

Mr. Dan Bature yace rundunar 'yansanda zata samar da cikakken tsaro ga dukan jam'iyyun siyasa lokacin neman zabe da kuma ranar zaben. Yayi wannan furucin ne a jihar Ondo, jihar da za'a gudanar da zaben gwamna watan gobe yayinda ya kai ziyara.

Ya bukaci jami'an 'yansanda dake kula da kananan hukumomi da su sa ido soasi kada su bari jami'an dake karkashinsu su wuce makadi da rawa a wajen gudanar da ayyukansu.

Dangane da binciken takardun ababen hawa da 'yansanda keyi a kan hanyoyi, Mr. Dan Bature yace su bari domin ba aikinsu ba ne kuma duk dansandan da ya cigaba da yin hakan har aka kamashi zai fuskanci hukumci.

Ga rahoton Hassa Umaru Tambuwal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Aikin 'Yansanda Ba Ne Sun Shiga Harkokin Zabe ko Su Binciken Takardun Ababen Hawa -1' 37"