Har yanzu tsugune ba ta kare ba a kan batun yiwuwar samun sauki a farashin mai a Najeriya duk da cewa wasu ‘yan kasar na ci gaba da bayyana yakinin cewa shigowar tattacen man matatar Dangote a gidajen man kasar zai iya rage tsadar da ake fama da shi, masana sun ce ba lallai ba ne hakan ya yi sanadin rage farashin kowace lita ba, saidai idan har gwamnati za ta rika saya ta rage kudin ta hanyar biyan tallafi.
‘Yan Najeriya dai sun kosa su fara ganin ana rarraba tataccen man fetur na matatar man Dangote zuwa ga gidajen mai a fadin kasar, lamarin da su ke ganin zai kawo sauki gare su, inda suke neman bayani a kan takamaiman lokacin da hakan zai kasance zahiri a yayin da suke ci gaba da kokawa a kan yadda tsada da karancin man ke tasiri ga yanayin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
Matashi, Kabiru Abdul dai ya bayyana cewa tsadar mai ta ninka kudin mota da ya ke biya zuwa wajen aiki sama da sau biyu; ya na mai cewa dole ne gwamnati ta dubi lamarin ta tausaya wa talakawa.
Shin yaushe ne ma za a fara ganin tataccen man matatar man Dangote a gidajen mai a Najeriya? Masani a fannin makamashi kuma Malami a jami’ar Nile dake birnin Abuja, Dakta Ahmed Adamu, ya ce ganin yanayin rashin tabbas a fannin albarkatun man, akwai yiyuwar a dan ja lokaci kafin a fara rarraba man Dangote a Najeriya.
A game da tsarin yadda man fetur daga matatar man Dangote zai iya kai ga dukkan sassan kasar, Dakta Ahmed Adamu, ya ce za a iya yin wannan aiki ta hanyoyi biyu da suka hada da ko kamfanin NNPCL ya rika sara ya rarraba wa ‘yan kasuwa ko a bai wa matatar Dangote dama ta kayyade farashinta.
Haka kuma Dakta Adamu ya kara da cewa ba lallai ba ne samun tataccen man matatar Dangote ya kawo sauki a farashin kowace litar mai ba.
Shin dilallan man fetur masu zaman kansu sun fara samun mai daga matatar man Dangote, shugaban kungiyar IPMAN, Alh. Abubakar Migandi Shettima, ya ce ba su da cikakken bayani a kan lodin shi kuma a shirye suke su yi cinikayya da matatar idan za ta yi aiki tare da su kai tsaye.
A karshen makon Jiya ne kamfanin NNPCL ya tabbatar da cewa dillalan man fetur karkashin kungiyar IPMAN zasu rika samun wadataccen mai, sai dai a yanzu mambobin kungiyar ba sa samun yadda su ke so kamar yadda Alhaji Maigandi ya shaida mana.
Duk da jitar jitar cewa akwai yiyuwar kamfanin NNPCL zai kasance dillalin man matatar Dangote ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu, babban jami’in yada labaran kamfanin, Olufemi Soneye, a cikin wata sanarwar da ya fitar, ya ce ba wannan maganar, kamfanin NNPCL bai ce shi kadai zai iya sayen mai daga matatar man Dangoten ba.
Saurari rahoton Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5