Ba A Bukatar Gabatar da Kudurin Takawa Muller Birki-Mitch McConnell

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai, Mitch McConnell

Shugaban jami’iyar Republican a majalisar dattawan Amurka Mitch McConnell yace mai yiwuwa ne ya takawa kudurin dokar da zata hana shugaba Donald Trump korar mai bincike na musamman Robert Muller birki.

McConnel ya fadawa manema labarai a jiya Talata cewa, kokarin da 'yan jam'iyar Democrat da Republican zasu yi na neman a kada kuri'a a kai bashi da wani amfani.

Yace shugaban kasa ba zai kori Robert Muller ba. Ya kuma kara da cewa suna da abubuwa da dama da ya kamata su kammala a cikin wannan shekara, amma ba kada kuri’a a kan abin da bashi da amfani ba.

Wakilin jihar Arzona a majalisar dattawa dan Republican mai barin gado Jeff Flakes da ya zauna a kan kwamitin shari’ar majalisar, ya yi barazanar hana wadanda Trump zai nada a sashen shari’a idan McConnell bai yarda majalisar dattawa ta kada kuri’a a kan kudurin Muller ba.

Shiko shugaba Trump ya ci gaba da caccakar bincike da Muller ke yi a jiya Talata. Ya aike da sakon Tweeter yana cewa kafofin yada labarai sun maida Muller tamkar wani mutumin kirki alhalin akasin hakan ne.