Shugaba Buhari wanda ya samu wakiltar hafsan hafsoshin Najeriya Janar Abayomi Olorunshakin yace ko shakka babu idan ta kama a karawa sojojin kasar wa'adi a yakinsu da Boko Haram gwamnati zata yi hakan ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban yana magana ne a taron karshen shekara na sojojin Najeriya da suke yi a Dutse fadar gwamnatin Jigawa wanda kuma zasu kammala Juma'a mai zuwa. Makasudin taron dai domin duba nasarori da kalubale da sojojin suke fuskanta ne a yaki da 'yan Boko Haram da kuma duba sauran batutuwan tsaro.
Shugaba Buhari yace ayyukan kungiyoyin ta'ada sun zama ruwan dare gama duniya musamman idan aka yi la'akari da hare haren kunar bakin wake na kwana kwanan nan a kasashen Mali da Faransa.
Kalamun shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka Barack Obama yake kira ga al'ummar musulmin duniya da su kara kaimi wajen yaki da kungiyoyin 'yan tarzoma kamar kungiyar ISIS dake haddasa rikici a kasashen Syria da Iraqi.
Dangane da ko rundunar sojojin Najeriya zata nemi karin lokaci akan yakinta da Boko Haram babban hafsan sojojin Janar Buratai yace har yanzu suna fata zasu cimma burin kawo karshen Boko Haram a wannan watan. Idan basu cimma burinsu ba to sai lokacin ya kai kafin su kara magana a kai.
Manjo Janar Alwali Kazir tsohon babban hafsan mayakan Najeriya yace ba abu ne sabo ba a baiwa sojoji wa'adi a fagen yaki. Yace idan za'a tura soja yaki dole ne a bashi lokacin gamawa. Shi kuma zai yi kokari ya yi aiki ya cika lokacin. Idan bai cika aikin ba cikin lokacin da aka bashi kamata ya yi ya nemi kari.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5