Ayuba: Wakoki Na Suna Kira Ga Matasa Babu Bangar Siyasa

Ayuba Ahmad

Ayuba M Ahmad, wanda aka fi sani da 'Waka ce' — mawakin soyayya ne da fadakarwa, wanda ya ce mafi yawan wakokin sa na fadakarwa ne. A 'yan kwanakin nan ma, ya shirya wata waka ta fadakar da matasa dangane da harkokin siyasa.

Mawakin dai ya ce sunan wakar ta sa dai 'Ranar Biyan Bukata’ wacce ta ke nusar da matasa yadda 'yan siyasa kan yi wasa da hankalin matasa, wajen cimma burikansu na kashin kansu, tare da nuna halin ko in kula ga yadda kasa ke tafiya, musasaman na matsalolin da suka shafi al'umma.

Ya kara da cewa a bangaren nanaye ma shima fadakarwace duk da cewar wakokin nanaye na dauke da kalamu na soyayya, alal misali a wata wakar sa mai suna ‘Gauraye’ wacce yayi wa samari da suka gaza yin aure akan lokacin da ya dace.

Babban abinda ya ke ci masa tuwo a kwarya ba kamar na sauran mawaka ba ne, a gida bai samu matsala ba sai dai da abokansa wadanda suke nuna masa kishi da hassada dangane da zabinsa a fagge na waka.

Ya ce babban alfanun da ya samu dai sun hada da samun abin duniya, sannan yana da burin waka ta kai shi inda kafarsa ba zata iya zuwa ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Ayuba: Wakoki Na Suna Kira Ga Matasa Babu Bangar Siyasa 4'50"