Assalamun Alaikum da fatan mai saurare yana cikin koshin lafiya. Cikin labaran wasannin namu na yau za mu duba batun wasannin motsa jiki ne da ke gudana a Birnin Bamingham na kasar Ingila da kasashen rainon ingila ke fafatawa a tsakaninsu.
Zamu kawo muku jerin kasashe guda goma da suka sami yawan lambobi da suka hada da Zinare, Azurfa da kuma Tagulla. Ya zuwa yau Alhamis hudu ga watan Agustan shekarar da muke ciki ta 2022.
Kasar dake ta daya a yawan lambobi ita ce, Australiya mai lambobi guda 123, sai mabi mata, mai masaukin baki kasar Ingila mai lambobi guda 104. kasar Kanada ce ta uku da lambobi guda 57, sai kasar New Zealand ta hudu da lambobi guda 35. Kasa ta biyar kuwa, ita ce Scotland mai lambobi guda 32.
Ta shida a jerin kasashe goma wadanda suka sami lambobin, ita ce Afrika Ta Kudu mai lambobi guda 19; ta Bakwai Indiya, mai lambobi guda 18, sai kuma Wales da ta zo na Takwas da yawan lambobi guda 14; Kasar Malesiya ta zo na tara da yawan lambobi guda Takwas, sai na goma Najeriya, itama dai tana da lambobi guda Takwas kamar Kasar Malesiya, saidai banbancin a yawan Azurfa ne. A yayin da kasar Malesiya ke da guda biyu, Ita kuwa Najeriya guda daya take dashi.
Bari kuma mu waiwayi rikicin hukumar kwallon kafar kasar Najeriya wato NFF da kuma tsohon Kocin Super Eagles, Gernot Rohr. Tsohon Kocin, ya ce a dole kanwar na ki, hukumar kwallon kafar Najeriya ta biya shi Naira Miliyan 157, da kuma kudin ruwa, a matsayin kudadensa na albashi da ba a biya ba, sanadiyyar gibi na rashin biyan albashin. Gernot Rohr, ya kai karar hukumar kwallon kafar Najeriya ne gaban hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA, data umurci hukumar kwallon Najeriya da ta biya Gernot Rohr , kudadensa nan da kwanaki 45 ko kuma a jefa mata takunkumi.
A halin da ake ciki kuma ,Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya umurci hukumar Kwallon kafar kasar wato NFF, da ta gudanar da zaben shugabannin hukumar a yayin da wa’adin shugabannin ke karewa a watan gobe na Satumba.
Shugaba Buhari ya bukaci ganin an yi kwaskwarima ga tsarin shugancin hukumar domin sanya dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tamaula
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad:
Your browser doesn’t support HTML5