Australia Da New Zealand Za Su Karbi Bakuncin Gasar Kwallon Kafar Cin Kofin Duniya Ta Mata Ta 2023

  • Murtala Sanyinna

Shugaban FIFA Gianni Infantino

Kasashen Australia da New Zealand ne za su karbi bakuncin gasar kwallon kafar cin kofin duniya ta mata mai zuwa a shekara ta 2023, bayan da suka sami gagarumin rinjayen kuri’un da aka jefa a takarar karbar bakuncin gasar.

Hadin gwiwar kasashen 2 sun yi galaba akan Colombia da ita ma ta so karbar bakuncin gasar, wadda ita ce ta farko da aka fadada ta zuwa kasashe 32 da za su fafata.

Japan wadda ke cikin takarar a da, ta janye a ranar Litinin, bayan da rahoton wani kwamitin hukumar FIFA ya bayyana cewa matsayin shirin ta ya na kasa da na wadannan kasashen.

Da farko an yi hasashen zaben zai yi zafin gaske domin an yi tsammanin wakilan kasashen Turai za su goyi bayan Colombia, to amma kuma sai aka sami rata mai yawa a kuri’un, inda Australia da New Zealand suka sami kuri’u 22, yayin da Colombia ta ke da 13.