Auren Dole Ne Yayi Sanadi

Wata matashiya Dausiya Abdulmumini,mai shekaru goma sha biyar (15) ta kashe mijinta Saminu Usman, mai shekaru ashirin da bakwai (27) har lahira, a kauyen unguwar dan Mayaki, dake karamar hukumar Bakori a cikin jihar Katsina.

Ita dai wannan matashiya tace ta aikata hakan ne sabili da cewa tana da wanda take so amma aka tilasa ta auri Saminu abinda tace bayi mata dadi ba sai ta yanke shawarar sa masa maganin bera a cikin abinci ya ci yamutu kuma wani dan uwanta ya ci abinci shima ya cika.

Amma wata ‘yaruwar mijinta Shafa’atu Usman, mai shekaru ashirin da uku (23) da ta ci loma uku acikin abinci Allah yasa tana da sauran shan ruwa ta rayu bayan da aka yimata magani a asibiti.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Katsina Benson Gwana, wanda ya gabatar da Dausiya da wasu bata gari ga manema labarai, yace rundunar zata cigaba da tabbatar da ganin cewa ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a.