Alhamis tarayyar Afirka ta tara sama da dala milyan 350 a taron neman gudamawa domin tallafawa bala’in fari da ‘yunwa da suke addabar wasu kasashe dake kuriyar Afirka.
Shugaban majalisar gudanarwar kungiyar Jean Ping, ya gayawa manema labarai cewa gudamawar da aka bayar sun hada da dala milyan 300 da bankin raya kasa ta Afirka ta bayar, san nan dala milyan 51 daga wasu kasashen Afirka da kuma wasu kafofi.
Kungiyar tarayyar Afirka ta sha suka sabo da sanyin jikinta kan bala’in fari da ‘yunwa da suka tilastawa dubun dubatan ‘yan kasar Somalia gudu daga gidajensu domin neman abinci da ruwa.
Kamin kaddamar da shirin neman gudamawar na jiya Alhamis, dala dubu dari biyar kacal ne kungiyar mai kasashe 54 ta ayyana domin tallafawa shirin shakwo kan bala’in a kuriyar Afirka.
Akalla shugabnin Afirka hudu daga yankin da bala’in yafi barna ne suka halarci taron.