Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uwargida Gadhafi Da 'Yayansu Uku Sun Tsere Zuwa Aljeriya


Tabarmar kofa mai hoton Kadhafi da 'yan tawaye suke amfani da shi.
Tabarmar kofa mai hoton Kadhafi da 'yan tawaye suke amfani da shi.

A safiyar jiya litinin, ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta bada labarin cewa uwargidan shugaban Libya Safiya Moammar Gadhafi, da ‘ya’yansa uku,Aisha da Mohammed da Hannibal, sun tsallaka kan iyaka da mota suka suka shiga Aljeriya.

A safiyar jiya litinin, ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta bada labarin cewa uwargidan shugaban Libya Safiya Moammar Gadhafi, da ‘ya’yansa uku, Aisha da Mohammed da Hannibal, sun tsallaka kan iyaka da mota suka suka shiga Aljeriya.

Shugabannin ‘yan tawayen Libya suka ce zasu bukaci hukumomin Aljeriya da su tusa musu keyarsu zuwa Libya.

Jami’an Aljeriya suka ce sun shaidawa babban sakataren majalisar dinkin Duniya da majalisar gudanawar ‘yan tawaye wannan bayanan. A baya jami’an ‘yan tawaye sun zargi Aljeriya makwabciyar Libya daga arewaci ita kadai ce bata amince da majalisar ‘yan tawayen ba, kuma tana goyon bayan Gadhafi har da samar mishi sojojin haya da nufin murkushe bore da ake masa. Aljeriya ta musanta wan nan zargi.

Har yanzu babu labarin inda shugaban na Libya yake, da wasu daga cikin ‘ya’yansa maza. Manyan ‘yan tawaye jiya litinin suka bada labarin cewa sai ta yiwu an kashe dan shugaban kadhafin Khamis,kwamandan rundunar soji ta musamman, a wani artabu da aka yi ranar Asabar a kudancin birnin Tripoli. An sha bada labarin mutuwarsa sau tarin yawa tun barkewar rikicin kasar, amma an kasa tabbatar da haka.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG