Atusayen Cikar Shekaru Sittin Da Kafa Rundunar Sojojin Ruwan Najeriya
Wani sojan ruwan Najeriya tsaye jikin wata bindiga a kan jirgin ruwan yakin Najeriya lokacin wani atusayen mayakan ruwan kasashe dabam-dabam, mil 50 daga bakin gabar Lagos, Jumma'a 27 Mayu, 2016.
Wani sojan ruwan Najeriya tsaye jikin wata bindiga a kan jirgin ruwan yakin Najeriya lokacin wani atusayen mayakan ruwan kasashe dabam-dabam, mil 50 daga bakin gabar Lagos, Jumma'a 27 Mayu, 2016.
Babban hafsan mayakan ruwan Najeriya, Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, yana kallon atusayen mayakan ruwan kasashe da dama a ranar alhamis, 26 Mayu 2016, kimanin mil 50 daga bakin gabar Lagos.
Wani jirgin ruwan yaki na Faransa da ya shiga cikin atusayen mayakan ruwan kasashe da dama tare da na Najeriya a ranar Jumma'a 27 Mayu, 2016.
Sojojin ruwan Amurka da na Najeriya su na shirin shiga wani jirgin yakin Najeriya mai suna NNS Burutu domin atusaye a dab da gabar Najeriya, a wannan hoton da aka dauka tun ranar 13 Fabrairu 2010.
JIrgin yakin Amurka mai suna USS Barry, a lokacin da ya shiga cikin bukin da aka yi na baya na cikar shekaru 50 da kafa rundunar sojojin Najeriya a bakin tekun Lagos a ranar Jumma'a, 2 Yuni, 2006.