Attoni-Janar din Amurka William Barr na fuskantar tambayoyi daga ‘yan majalisar dokoki a yau dinnan Laraba, bayan fitar da rahoton mai bincike na musamman na Robert Mueller a farkon wannan watan, kan binciken katsalandan din Rasha a zaben shugaban Amurka na shekarar 2016.
Barra zai gana da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Shari’a mai rinjaye ‘yan Republican, na tsawon a kalla sa’o’i uku.
Bashakka Barr zai fuskanci tambayoyi game da wani rahoton jaridar Washignton Post na jiya Talata mai cewa Mueller ya tuntubi shi Attoni-Janr din ta waya da kuma ta wasika, inda ya bukaci Barr ya saki takaitaccen bayanin da kwamitin binciken da ya rubuta kan rahoton, amma a maimakon haka Barr ya saki nasa takaitaccen bayanin, wanda Mueller ke ganin bai kunshi muhimman batutuwa ba, da yanayin rahoton da kuma manufar rahoton na karshe.