Atone-Janar Na Amurka Ya Fitar Da Takaitaccen Rahoton Mueller

Robert Mueller

Atone-janar na Amurka Bill Barr ya fitar da takaitaccen bayanin rahoton kwamitin bincike na musamman da jigon bincike na musamman Robert Mueller ya jagoranta.

Rahoton da aka dade ana jira, a kan ko kwamitin yakin neman zaben Donald Trump ya hada baki da Rasha a zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da goma sha shida.

Ga muhimman batutuwa da rahoton da aka gudanar na tsawon shekaru biyu ya kunsa, wanda kuma shugaba Trump ya yi ta nanatata cewa, bita da kulli ne kawai ake yi mishi, tare da cewa sakamakon binciken ya wanke shi.

Hada Baki

Kwamitin na Mueller ya gano cewa babu wata takamammar shaida da ta nuna cewa, Rasha tayi katsalandan a zaben, ko ta hanyar cusawa al’umma labarun karya ko kuma yiwa email din tawagar yakin neman zaben Hillary Clinton kutse.

A cikin wasikar da ya aikawa majaliasar dokokin Amurka, Barr yace, kwamitin binciken na Mueller ya gano cewa, wadansu mutane dake da alaka da Rasha sun yiwa ofishin yakin neman zaben Trump tayin bayanai har sau biyu da zummar taimaka wa kyamfen din na Trump.”

Sai dai Barr ya ambaci rahoton Mueller kai tsaye da yace, Kwamitin binciken “bashi da tabbacin cewa, jami’an yakin neman zaben Trump sun hada baki ko kuma aiki tare da gwamnatin Rasha a katsalandan da tayi a zaben.”

Babakere

Masu sa ido da dama sun yi harsashen cewa, babban abinda yake da hadari ga Trump shine zarginshi da yin babakere da hana doka aikinta, musamman dangane da korar darektan hukumar binciken manyan laifuka ta FBI- watau James Comey da ya yi wanda yake jagorantar binciken kafin a nada kwamitin Mueller.

Sai dai Barr yace, shaidar da aka zayyana a rahoton na Mueller bata isa ta zama hujjar cewa shugaba Trump ya hana doka aiki ba.

Barr ya kara da cewa, “Idan aka dubi matakan da shugaban kasar ya dauka, wadanda da dama ya dauka a gaban idon jama’a, rahoton bai bai nuna wani matakin da aka dauka, da a ganinmu, ya nuna yin babakere da hana doka yin aikinta ba.”

Sai dai yayinda, Barr, wanda shugaba Trump ya nada shi, ya yanke hukumci cewa, shugaban bai hana doka yin aikinta ba, ya bayyana cewa, rahoton na Mueller bai yanke hukumci dangane da batun hana doka aikinta ba.

“Sabili da haka, kwamitin na musamman bai nuna wata matsaya a kan batun ba, bai nuna shugaban ya hana doka yin aikinta ba, kuma bai wanke shugaban kasar ba.”

Babu Sauran Zarge-Zarge da za’a yi

Tsohon mai ba Trump shawarwari kan harkokin tsaron kasa,Mike, Flynn, da tsohon lauyanshi MIcheal Cohen, da kuma tsohon shugaban yakin neman zabensa, Paul Manafort, suna daga cikin mutane 34 da kwamitin na Mueller ya samu da laifi, sai dai sune zasu zama na karshe, a bisa ga cewar Barr.

“Rahoton bai bada shawarar sake tuhuma, ko kuma ya kunshi wadansu tuhume tuhumen da ba a riga an bayyanawa jama’a ba,” bisa ga cewar Barr a wasikar da ya aikawa shugabannin kwamitocin harkokin shari’a na majalisun dattijai da na wakilai.

(Karin bayani daga AFP)

Fashin Baki Kan Rahoton

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Aminu Yakubu Lame, wani dan Najeriya da ya shafe kusan shekaru talatin a Amurka, wanda kuma yake sa ido sosai a harkokin siyasar kasar, ya yi fashin baki kan rahoton da aka fitar, inda ya bayyana cewa, zai yi wuya a hukumta Shugaba Trump dangane da batun hada baki kasancewa babu wani bayani da ya nuna ko dai yana da masaniya ko kuma tare da hadin bakinsa aka nemi hadin kan Rasha, ko kuma aka hada baki da gwamnatin kasar Rasha wajen yin katsalandan a zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da goma sha shida.

Saurari cikakken bayanin nasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Aminu Yakubu Lame Kan Rahoton Mueller-4:00"