A jiya Laraba, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi allawadai da harin jirgin saman da aka kai a Sokoto wanda ya hallaka kimanin mutane 10.
Da yake martani a kan lamarin a sakon da ya wallafa a shafinsa na X a yau Alhamis, Atiku ya ce "mummunan harin jirgin saman da ya yi sanadiyar salwantar gwamman rayuka a garuruwan gidan Sama da Rumtuwa na jihar Sokoto da ke zaune cikin lumana, abin takaici ne da ya zamo wajibi ayi tir da shi da kakkausar murya."
Tsohon mataimakin shugaban kasar na mamakin yadda aka kasa daukar darasi daga harin jiragen saman da aka taba kaiwa kauyen Tudun Biri da ya hallaka fiye da mutane 80 a watan Disamban bara.
Yayin da yake amincewa da halascin kaiwa 'yan ta'adda hari, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce, "wajibi ne a rika kai irin wadannan hare-hare cikin matukar kwarewa da sahihan bayanan sirri."
A yayin da gwamnatin jihar Sokoto ke cewa harin jirgin saman da sojojin suka kai ya hallaka kauyawan da basu ji ba basu gani ba, rundunar sojin Najeriya ta dage a kan cewa harin a kan mambobin kungiyar 'yan ta'addar Lakurawa ne.