Atiku Ya Sha Alwashin Lashe Zaben 2019

Atiku Abubakar

Tshohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana kwarin gwiwar cewa shi zai lashe zaben shugaban kasa da za'a yi ranar Asabar mai zuwa.

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin lashe zaben shugaban kasar da za’a gudanar ranar Asabar mai zuwa, sannan ya ce kushe mulkin jam’iyyar PDP na tsawon shekaru 16 cewa ba ta yi komai ba soki burutsu ne.

Ya bayyana hakan ne a wurin taron majalisar koli na jam’iyyar PDP da aka yi a shelkwatarta da ke Wadata Plaza a Abuja.

Taron na su, ya duba tasirin dage zaben makon jiya da kuma shan alwashin komawa bakin dagar kamfen.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, a lokacin da yake jawabi ya nuna tamkar Atiku shugaban kasa ne mai jiran gado da yardar Allah bayan zaben ranar Asabar mai zuwa, inda ya nuna gazawar gwamnati Buhari ta APC zai ba su dama su lashe zaben.

Dukkan wadanda su ka yi jawabi a gurin taron sun caccaki kalaman shugaba Buhari na daukar matakin gamawa da duk wanda aka samu da satar akwatin zabe, inda su ka ce hakan tamkar bai wa sojoji umarnin kashe masu zabe ne.

A martanin da jam’iyyar APC mai mulki ta mayar ta hannun wani wanda shugaba Buhari ya karba kwananan, Bala Bello Tinka, ya ce duk da juya manufar kalaman shugaban, amma suna kan hanya, sannan ya yi kira da shugabannin ‘yan adawa da su yi wa shugaban adalci.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Atiku Ya Yi Alwashin Lashe Zaben Shugaban Kasa