Atiku Abubakar Ya Gana Da Wadansu ‘Yan Majalisar Dokokin Amurka

Alh. Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyar hamayya a Najeriya PDP, Alh Atiku Abubakar yana ziyara a Amurka inda ya gana da wadansu ‘yan majalisar dokokin kasa, yayinda a yau yake shirin zuwa ma’aikatar harkokin wajen Amurka

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, jim kadan bayan fitowarshi daga majalisar dokokin Amurka, Alhaji Atiku ya bayyana cewa, ya tattauna ne da ‘yan majalisar kan abubuwan da suka shafi Najeriya da kuma dangantakar da Najeriya take so ta karfafa tsakaninta da sauran kasashen duniya, musamman Amurka.

Alhaji Atiku wanda yace ya zo Amurka ne bisa gayyatar wadansu kungiyoyi dabam dabam, ya kuma bayyana cewa, yana shirin kai ziyara ma’aikatar harkokin wajen Amurka inda zai tattauna da wadansu jami’ai, daga nan kuma ya gana da ‘yan kasuwa.

Dan takarar na jam’iyar PDP yace ziyarar tasa a Amurka manuniya ce cewa, babu gaskiya a cikin abinda ake fadawa mutane game da shi, yace ziyarar da ya kawo zata kara farfafawa wadanda har yanzu suke da shakku cewa, bashi da wani tabon da ya hana shi zuwa Amurka.

Ya bayyana cewa, Amurka a shirye take ta marawa kowacce kasa da take bin tafarkin damokaradiya baya, sabili da haka ya hakikanta cewa, tana tare da Najeriya a kokarin kasar na kare damokaradiya.

Saurari cikakken bayanin, Alhaji Atiku Abubakar a hirarsu da Aliyu Mustapha Sokoto

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar Atiku A Amurka-3:00"