A wani yanayi na ba zato ba tsammani a ranar Dimokradiyya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fuskanci wata ‘yar matsala a lokacin da yake yunkurin hawan wata mota kirar a kori-kura domin zagayawa da shi dandalin Eagles Square a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Lamarin ya faru ne a yayin bikin ranar Dimokuradiyya a yau Laraba 12 ga watan Yunin 2024 wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya zuwa duk ranar 12 ga watan Yunin shekara-shekara sabanin ranar 29 ga watan Mayun da aka saba a baya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP ya bayyana alhininsa a shafinsa na Twitter wanda aka sani da (X), inda yake cewa:
"Ina mika sakon alhini da jajantawa ga shugaban kasa Bola Tinubu, bisa wannan mummunan al'amari da ya faru yayin da yake shirin sake duba faretin bikin ranar dimokuradiyya. Ina fatan yana cikin koshin lafiya”, inji Atiku
Shima Sanata Shehu Sani da yake bayyana nashi alhini a dandalin na X, ya jajanta yana mai cewa:
"Ba wai kawai Shugaba Tinubu ba, duk wanda ke raye zai iya zamewa ya fadi; hakan ya faru da Shugaba Biden da Fidel Castro. Shugabanni mutane ne kamar kowa" in ji sanata Shehu Sani
Faifan bidiyon yadda shugaban ya zame, ya haifar da cece kuce da muhawarori a dandalin kafafen zamani da dama, inda mafiya wasu ke tausayawa da jajantawa shugaban yayin da wasu ke nuni da sabanin haka.
Wani lamari na ban mamaki shine yadda ‘yan Najeriyan da dama suka tausayawa shugaban duk da halin tsananin matsi da ake ciki wanda masu sharhi suke gani zai iya tunzura ‘yan kasar wajen nuna halin ko in kula da lamarin da ya faru da shugaban, sabanin haka, mutane da dama sun nuna dattaku da jan hankalin cewa babu shakka shugaban dan Adam ne, kuma hakan zai iya faruwa da kowa, tare da yiwa shugaban addu’ar Allah ya kiyaye na gaba.
Tuni dai fadar shugaban kasar ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar wa al’ummar kasar cewa shugaban bai sami rauni ba kuma ya cigaba da gabatar da harkokin gwamnati na yau da kullum bayan ‘yar karamar zamewar.
~Yusuf Aminu Yusuf ~