Asusun IMF Zai Tallafa Wa Kasar Ghana

Shelkwatar Asusun bada lamuni ma duniya

Asusun bada lamunin kasa da kasa IMF ya kammala ganawa da gwamnatin Ghana tare da jaddada aniyarta na tallafa wa kasar.

A cikin rahoton da ta fitar, IMF ta amince cewa mamayar da Rasha ke yi a Ukraine tare da annobar covid 19 na daga cikin abubuwan da suka sanya kasar cikin mawuyacin hali

Asusun IMF dinnan bayan kammala ganawa da masu ruwa da tsakin ya bayyana cewa, ashirye yake ya tallafawa Ghana yayin da kasar ta tsunduma cikin wanan mawuyacin halin na raunin tattalin arziki.

Asusun ya kuma ce ya tattara duk wasu bayanan da yake bukata domin gano taimakon da Ghana ta cancanta da ta samu daga IMF.

Wasu masana na hasashen cewar Ghana zata samu tallafin IMF daga kwatan badi wato 2023 amma kuwa kudaden kasashen waje da Ghana ta adana a gidauniyarta dake babban bankin kasar ba zai iya tsallake wannan shekara zuwa 2023 ba.

To sai dai ba wannan ne karon farko da gwamnatin Ghana ta tinkari IMF ba. Ta fara tun shekarar dubu da dari tara da casa'in da tara a inda ta samu tallafin da ya kai dala biliyan 1.96 . wannan ne karo na biyar da IMF ta ke tallafawa kasar .

Saurari cikakken rahoton Hamza Adams cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Asusun IMF Zai Tallafa Wa Kasar Ghana-3:00"