Rahoton wanda wata cibiya mai suna Capdoc.com ta fitar, wanda ke kula da yadda ake ayyukan samar da kiwon lafiya a India, ta ce kimanin mutane dubu biyar ne daga Najeriya suka je neman magani a bara a kasar ta India.
Sanarwar rahoton wacce shugaban wannan cibiya Mr Sora Maskara ya fitar, ya ce aksarin masu neman maganin, na ta’allaka ne wajen neman magungunan cututtukan da suka shafi ciwon zuciya da kashi da hanta ko kuma daji.
Dr Aminu Idi, likita a Najeriya ya ce dalilin da ya sa ake zuwa neman magani a irin wadannan asibitoci da ke ketare shine babu wani mai kudi ko gwamnati da ta kafa irin wannan asibiti a Najeriya.
“Sannan na biyu irin wadanda za su iya taimakawa kamar banki, tsarin karbar bashinsu ba ya taimakon likitoci hade kuma da matsalar magungunan jabu.” In ji Dr Idi.
Sai dai daga cikin dalilin da masu neman maganin ke bayyana na zuwa India shi ne “na daya dai suna da kwararrun likitoci sannan kuma suna da kayan aiki na zamani, kuma suna da dan arha.” In ji Malam Usman, wani da yanzu haka yake karbar magani a kasar ta India.
Ga karin bayani a wannan rahoto na Babangida Jibril daga Legas:
Your browser doesn’t support HTML5