Asara Ce Ga Musulmi Ya Yi Sakaci Da Albarkar Ramadan

Malama Ibrahim Abubakar Tofa

Har yanzu muna nan a kan fatawar malamai dangane da alfanun aikata ayyukan alkhairi a lokacin azumi da ire iren lada da albarakar da ke cikin wannan wata inda aka bukaci musulmi da su kwatanta aikata daya daga cikin ayyukan ibada domin samun rahama

Limamin masallacin Juma’a na Kuba da ke Tukuntawa kuma sakataren majalisar malamai ta jihar Kano, Malam Ibrahim Abubakar Tofa ya bayyana haka ne a wata zantawa da wakiliyar DandalinVOA inda ya ce, watan Ramadana wata ne da ake daure shaidanu kuma ake ribanya ladan da Musulmi ya aikata.

Ya ce babban abin takaici shi ne, watan Ramadana ya shigo mumini ya zauna bai ribanci albarkacin da ke cikin wannan wata ba.Ya ce, lallai mutum ya yi asara, domin kuwa lokaci ne da ake aikata ayyuka domin samun Aljanna.

Ya kara jan hankalin al’umma da su jajirce wajen yawaita sallah, da zikiri, da sauran ayukkan lada domin wata ne da ke zuwa sau daya a shekara kuma lokacin ne da Ubangiji ke yafewa bayinsa.

Daga karshe, ya ce mafi alfanun ayyukan da ake son mutum ya aikita sun hada da ciyarwa, mussaman ma a wannan lokaci na matsin rayuwa da ake fama da shi.

Saurari cikakken bayanin Mallam Ibrahim Tofa

Your browser doesn’t support HTML5

Malama Ibrahim Abubakar Tofa Ya Yi Kira Ga Alumma