Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya karbi daliban makarantar Kurigan da aka kubutar bayan kwashe kwanaki 16 a hannun 'yan-bindigan.
Gwamnan ya dage kan cewa dalibai 137 da malami daya 'yan-bindigan suka sace kuma gaba daya daliban sun dawo sai dai malaminsu ya rasu a hannun 'yan-bindigan tun a daji.
Tun daren Lahadi dai aka kawo daliban Kaduna sai dai sun kwana ne a hannun sojoji inda aka duba lafiyar su a asibitin sojan kafin danka su a hannun gwamnan jihar Kaduna a humkumance a ranar Litinin.
Babban kwamandan runduna ta daya da ke Kaduna, Manjo Janar, Mayirenso Saraso shi ne ya mika daliban ga gwamnan jihar Kaduna kuma ya yi bayanin yadda aka kubutar da su.
Ya ce aikin hadin gwiwa ta hanyar hada karfin soja da kuma lalama aka yi amfani da su wajen kubutar da wadannan dalibai na makarantar Kuriga bayan kwashe kwana 16 a hannun 'yan-bindigan.
Sojan Najeriya sun karbi daliban ne a cibiyar aikin soja da ke dajin Dansadau a jihar Zamfara kafin rako su zuwa Kaduna, duka daliban dai su 137 ne sai malamin su daya.
Shi kuwa gwamna Uba Sanin da ya karbi wadannan dalibai ya ce asalin adadin daliban da aka sace dama 137 ne ba 287 ba.
Iyayen daliban dai ba su halarci zaman karbar 'ya'yan nasu ba kuma ba a bai wa daliban damar magana da 'yan-jarida ba sai dai gwamna Uba Sani ya saki wani faifan bidiyo na ganawar shi da daliban a daren Lahadi inda ya yi musu tambayoyi.
Jimullar daliban makarantar Kuriga 137 ne aka kubutar 76 mata 61 maza sai dai 131 aka gabatarwa manema labaru saboda shida na asibiti ba lafiya sai kuma malamin daliban da ya riga mu gidan gaskiya.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5