Wata kotun Najeriya ta tuhumi mutum takwas da ake zargi da hannu cikin jerin munanan hare-haren da aka kai kewayen Abuja babban birnin kasar.
Lauyoyin gwamnati masu shigar da kara sun ce wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne, kungiyar da ta dauki alhakin kai wasu munanan hare-hare a Najeriya kuma an dora ma ta laifin kai wasu dimbin hare-haren.
Ana zargin mutanen takwas da taka rawa cikin wasu hare-hare hudu da aka kai daban-daban tsakanin watannin Maris da Yuli wadanda su ka halaka mutane kimanin 25. Hari mafi muni shi ne wanda aka kai kan wani ofishin hukumar zabe a garin Suleja a cikin watan a Afrilu wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum goma sha shidda.
Wadanda ake zargin ba su amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa ba lokacin da su ka bayyana a yau talata a gaban wata kotun majistare a Abuja.
Shugaba Goodluck Jonathan ya yi alkawarin yin birki ga jerin tashe-tashen hankulan siyasa da na addinin da ke addabar Najeriya, amma har yanzu bai samu wata nasarar a zo a gani ba.
A jiya litinin wasu mahara sun afkawa wani ofishin 'yan sanda a garin Misau da ke jahar Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya inda su ka halaka mutum biyar.
Kungiyar Boko Haram ce ta dauki alhakin kai hare-haren watan jiya kan helkwatar Majalisar Dinkin Duniya a Abuja da kuma wani harin a watan Yuni da aka kai kofar helkwatar 'yan sandan Najeriya. Kungiyar so ta ke yi ta kafa tsarin mulkin shari'ar addinin Islama a yawancin sassan arewacin Najeriya.
Saboda irin wannan tashin hankali da ke faruwa a kasar, ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya bukaci Amurkawan da ke can da su kara maida hankali musamman ma a wuraren ibada da kuma inda jama'a ke taruwa.