Tsohon Kocin Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya nesanta kansa daga rade-radin da ake cewa, yana cikin masu gwagwarmayar neman zama mai horar da 'yan wasa na Real Madrid.
A cikin wata hira da ya yi da manema labarai, Wenger mai shekaru 69, a duniya ya ce, ba shi da wata masaniya ko tabbacin inda zai tsinci kansa a
shekara mai zuwa, amma ban da kocin Real Madrid.
Wenger ya ba da tabbacin komawa fagen horar da wasa a 2019, in da ya bayyana cewa, yana da cikakken dabaru kuma a shirye yake da ya koyar da irin dabarun nasa a kwallon kafa.
Ya zuwa yanzu Real Madrid ba ta nada koci na din-din-din ba, hakan ne ma ya sa Santiago Solari ke ci gaba da jan ragamar kocin na rikon kwarya.
Ku Duba Wannan Ma Dan Wasan Tottenham Dele Alli Ya Sabunta KwantiraginsaSolari wanda tsohon dan wasan Real Madrid ne kafin a ba shi rikon, shi ne kocin kulob din matasa na Real Madrid (Team B), inda ya fara jagorantar kungiyar a wasanta na farko da kafar dama domin kuwa sun doke UD Melilla da kwallaye 4-0 a gasar Copa de Rey.
Solari ya karbi ragamar kungiyar ne bayan Real ta sallami Julen Lopetegui a ranar Litinin bayan kashin da suka sha a hannun Barcelona a was an El-Classico.
Ana tsamanin Arsene Wenger zai koma da aikinsa na mai horas da 'yan wasa a farkon shekarar nan kamar yadda ya bayyana.