Arsenal Ta Lashe Gasar FA

  • Murtala Sanyinna

Arsenal ta lashe gasar FA ta Ingila

Arsenal ta lashe gasar kwallon kafa ta cin kofin FA na Ingila karo na 14, bayan ta doke Chelsea 2-1 a wasan karshe ta gasar a filin wasa na Wembley. 

Chelsea din ce ta soma zura kwallo a minti na 5 da soma wasan ta hanyar dan wasanta Christian Pulisic, wanda ya kafa tarihin kasancewa ba’amurke na farko da ya zura kwallo a wasan karshe na gasar ta FA.

Arsenal ta rama cin a minti na 28 ta hannun Pierre-Emerick Aubameyang a bugun finariti, kana kuma ya zurawa Arsenal din kwallon ta biyu a minti na 67.

Arsenal ta lashe gasar FA ta Ingila


Chelsea wadda ta soma wasan cikin damuwar rauni ga ‘yan wasanta da dama, ta yi ta kokarin farke cin na biyu, to amma hakan bai samu ba sakamakon korar da aka yi wa dan wasanta Mateo Kovacic a minti na 73 na wasan bayan da aka ba shi katin gargadi har sau biyu. Haka kuma an fitar da dan wasanta Pedro sakamakon rauni da ya samu a kafarsa.

Kocin kungiyar ta Arsenal Mikel Arteta ya lashe kofin na FA karo na 3 kenan a kungiyar, na farko a matsayin koci, yayin da ya lashe kofin a matsayin dan wasan kungiyar a shekarun 2014 da 2015.