Arsenal Ta Kammala Yarjejeniyar Sayen Sabbin 'Yan Wasa Biyu

Kungiyar kwallon Kafa ta Arsenal, ta cimma yarjejeniyar sayen ‘yan wasa guda biyu wanda hakan ke nuni da cewa sune ‘yan wasa cikon na uku wanda Kungiyar ta saye su a karkashin sabon kocinta Unai Emery.

‘Yan wasan dai sune Lucas Torreira, mai shekaru 22, dan wasan tsakiya na kasar Uruguay, mai taka leda a kungiyar kwallon Kafa ta Sampdoria, da kuma Guendouzi, shi kuma matashin dan wasan tsakiya ne daga kungiyar Lorient, mai shekaru 19, wanda dukan su ke kan hanya domin zuwa duba lafiyarsu a kungiyar Arsenal a ranar litinin 9/7/2018.

Kafin zuwan ‘yan wasan kungiyar Arsenal, tuni ta sayi dan wasan mai tsaron raga daga kungiyar Bayern Leverkusen, mai suna Bernd Lone.

Kungiyar kwallon Kafa ta PSG tana bukatar dauko dan wasan tsakiyar Barcelona Philippe Coutinho, mai shekaru 26, da haihuwa akan kudi yuro miliyan €270 kimanin fam miliyan £239 domin ya taimakawa dan wasanta Neymar, wajan samun nasarori a kulob din.

Shugaban kungiyar Real Madrid, Florentino Perez ya ce tuni ya zabi dan wasan Chelsea, Eden Hazard's a cikin jerin sunayen kungiyar Real Madrid zata yi amfani dasu a bana in har dan wasan ya amince ya dawo kulob din Madrid.

Manchester city ta amince da sayen dan wasan gaba na kungiyar Leicester city, Riyad Mahrez, akan kudi fam miliyan 60 inda dan wasan yake shirin zuwa gwajin lafiyarsa a kungiyar nan da awoyi 48.

Your browser doesn’t support HTML5

Arsenal Ta Kammala Yarjejeniyar Sayen Sabbin 'Yan Wasa Biyu